TASKAR KASAR HAUSA

Saturday, 3 September 2022

TASKAR ƘASAR HAUSA TA JAGORANCI BIKIN ƘADDAMAR DA SABBIN LITTATAFAN ADABI A JIHAR GOMBE

Bikin ya gudana ne a makarantar firamare ta Herwagana da ke garin Gombe a ranar Asabar 27 ga watan Augustar 2022, inda aka sami halartan jiga-jigan masana a harkar rubutu da masu yi wa Adabi hidima irin su; Alhaji Salihu Abdullahi (Jarman Kumo) wanda ya yi sharhi a kan littafin Siyasa Ba Da Gaba Ba. Sai Malam Dalhatu El-Nafaty wanda ya yi tsokaci a kan rubuce-rubuce a wannan zamani. A yayin da Malam Ibrahim Lamiɗo PhD wanda malami ne a jami'ar tarayya da ke Kashere, ya jaddada goyon bayansa ga marubutan tare da ƙarfafa musu guiwa. Sai Alhaji Kabiru Ibn Muhammad (Sarkin Doya) shugaba kuma babban daraktan gidan rediyo da talabijin mallakar jihar Gombe DG GMC shi ma ya yaba wa marubutan tare da jaddada goyon bayansa gare su.


Littatafan da aka kaddamar sun haɗa da; Siyasa Ba Da Gaba Ba wanda marubuta goma sha ɗaya suka yi hadakar samar da shi, sai Lu'ulu'u A Cikin Juji da Duniyar Audu na Rufai Abubakar Adam (R.A Adam), sai littafin Fitinar Zamani na Adamu Ahmed Yarma.

Daga ƙarshe an bayar da kyaututtuka ga marubutan da kuma manyan mutanen da suka halarci taron.





JERIN SUNAYEN MARUBUTAN DA SUKA RUBUTA SIYASA BA DA GABA BA
1. Rufai Abubakar Adam (R.A Adam)
2. Adamu Ahmed Yarma
3. Ayuba Muhammad Kumo
4. Ahmad Usman El-Nafaty
5. Usman Abubakar (Usman Flash)
6. Shehu T. Abdullahi
7. Rashidat Muhammad (Queen Rashoo) 
8. Zainab Hussaini
9. Aishatu Ibrahim Yahaya
10. Usman Umar Assakaafiy
11. Sunusi Musa