JARIDAR GASKIYA TAFI KWABO
Muhimman bayanai guda sha biyu (12) game da GASKIYA TAFI KWABO.
1. Ita ce jaridar
Hausa ta farko a Najeriya.
2. An kirkire ta a
shekarar 1939.
3. Ita ce jaridar
hausa mafi sanuwa a yammacin Afirka.
4. Ita ce jaridar
Hausa ta farko a duniya.
5. Ana buga ta sau uku
(3) a sati. Tana fitowa sau uku a sati.
6. Jaridar mallakin
gwamnonin arewa a karkashin kamfanin Gaskiya Corporation.
7. Ita ce Jarida ta
farko mallakin gwamnati a Najeriya.
8. Ta shahara wurin
kawo rahotanni Yakin Duniya Na Biyu II.
9. Babban hedkwatan ta
a Zariya.
10. Ita ce jaridar
cikin gida mafi jimawa a Najeriya, ta dauki tsawon shekaru saba'in tana aiki.
11. Tana bada
gudunmawa wajen gwagwarmayar yada kishin kasa da harshen Hausa.
12. Marubuci Dokta
Abubakar Imam ne Editan ta na farko