An haifi Aihaji Dr. Abubakar Imam, O.B.E; C.O.N.; LL.D (Hon.)
N.N.M.C. a shekarar1911a cikin garin Kagara sa’annan tana cikin Iardin Kwantagora,
yanzu kuwa Jihar Neja. Yayi makaranta a Katsina Training College kuma ya kama aikin
malanta a Makarantar Midil ta Katsina a shekarar 1932. Yana da shekara 22 ya rubuta‘RuwanBagaja’.
Ganin k’wazonsa wajen k’aga labara mai ma’ana yasa Dr. R.M. East shugaban OffishinTalifi
na Zariya ya roki a ba da shi aro daga Katsina yayi aikin rubuce rubuce a
Zariya.
Bayan ya koma
Katsina aka bi shi da rok’on ya kara rubuta wasu littattafan. A can ya rubuta‘Karamin
Sani k’uk’umi’cikin 1937. A cikin shekara 1938 sai Gwamnan Kaduna ya rok’a a
dawo da Dokta Imam Zariya a koya mashi aikin edita, ya zama editan jaridar
farko ta Arewa. Shine ma ya rada mata suna‘Gaskiya Ta Fi Kwabo’aka fara bugawa
a watan Janairu na shekara 1939.
Yayi shekara
12 yana wannan aiki na edita har ma ya rubuta wani littafi a lokacin
‘Yak’inDuniya Na Biyu’ watau‘Yak’inHitila’da yaba suna ‘Tafiya Mabudin Ilmi’.
Wannan littafi yaba da labarin tafiyarsa tare da wasu editoci na jaridun Afrika
ta Yamma zuwa ingila a jirginruwa a shekaran 1943.
Wani mashahurin littafi kuma da ya rubutashi ne
‘TarihinAnnabi da naHalifofi’ wanda aka fara buga shi a shekara 1957 lokacin
nan yana shugaban Hukumar ‘Daukar Ma’aikata ta Najeriya ta Arewa.
Aihaji Dr. Abubakar Imam shi aka fara nadawa Kwamishinan jin kararakin
Jama’a a shekara 1974 a Jihar Kaduna, lokacin ana kiranta Arewa ta Tsakiya. Ya rasu
yana da shekara 70 a duniya ranar Juma’a 19 ga watanYuni, 1981.
Alhaji Abubakar Imam ya rik’a cewa wannan aiki da yayi, na talifln‘Magana
Jari Ce’yayi masa amfani ainun. Ya kance wannan aiki shi ne ya bashi dammar zama
tare da mashahurin Baturen nan na talifin Hausa, Dr. R.M. East, O.B.E. Yace daga
gare shine ya koyi duk dan abin da ya koya na game da talifi. Abin mamaki, shi kuma
wannan Bature, Dr. East O.B.E., a wajen ‘Mukaddamar’ da yayi da Turanci tun farkon
buga ‘Magana Jari Ce’, ga abin da yace: ‘Muna godiya ga En’e ta Katsina,saboda taimakonsu,
da hangen nesa da sukayi, har suka yarda, suka bamu aron Malam Abubakar Imam. Suka
yarda, ya bar aikinsa, na koyar da Turanci a Midil ta Katsina, yazo nan Zariya,
yayi wata shida domin ya taimake mu, mu sami wadannan littattafai a cikin harshensa.
Iyakar abin da mu ma’aikatan wannan ofis mu kayi, na game da tailfin
wadannan littattafal, shi ne aiki irin na ofis, na shirya aI’amuran, yadda suka
kai har aka buga su. Ban da wannan salsu kuma taimakonsa da muka yi na tattara
masa’ littattafai iri iri, don ko zai kwaikwayi wani samfur. Saifa kuma wajen shiryawa
bayan da ya rubuta. ‘Kai, in dai har muna da wani abin da za mu yi kirarin munyi,
game da tailfin wadannan littattafai, to, babban abin kirarimmu kawai, shi ne
yadda mu kayi har muka binciko wannan malamin’.