TASKAR KASAR HAUSA

MARUBUCI DOKTA ABUBAKAR IMAM (Editan Arewa Na Farko) 1


An haifi Aihaji Dr. Abubakar Imam, O.B.E; C.O.N.; LL.D (Hon.) N.N.M.C. a shekarar 1911 a cikin garin kagara sa’an nan tana cikin Iardin Kwantagora, yanzu kuwa Jihar Neja. Ya yi makaranta a Katsina Training College kuma ya kama aikin malanta a Makarantar Midil ta Katsina a shekarar 1932. Yana da shekara 22 ya rubuta ‘Ruwan Bagaja’. Ganin k’wazonsa wajen k’aga labari mai ma’ana ya sa Dr. R.M. East shugaban Offishin Talifi na Zariya ya
roki a ba da shi aro daga Katsina ya yi aikin rubuce rubuce a Zariya.
            Bayan ya koma Katsina aka bi shi da rok’on ya k[ara rubuta wasu littattafan. A can ya rubuta ‘Karamin Sani k’uk’umi’ cikin 1937. A cikin shekara 1938 sai Gwamnan Kaduna ya rok’a a dawo da Dokta Imam Zariya a koya mashi aikin edita, ya zama editan jaridar  farko ta Arewa. Shi ne ma ya rad’a mata suna ‘Gaskiya Ta Fi Kwabo’ aka fara bugawa a watan Janairu na shekara 1939.
            Ya yi shekara 12 yana wannan aiki na edita har ma ya rubuta wani littafi a lokacin ‘Yak’in Duniya Na Biyu’ watau ‘Yak’in Hitila’ da ya ba suna ‘Tafiya Mabudin Ilmi’. Wannan littafi ya ba da labarin taflyarsa tare da wasu editoci na jaridun Afrika ta Yamma zuwa ingila a jirgin ruwa a shekaran 1943.
Wani mashahurin littafi kuma da ya rubuta shi ne ‘Tarihin Annabi da na Halifofi’ wanda aka fara buga shi a shekara 1957 lokacin nan yana shugaban Hukumar ‘Daukar Ma’aikata ta Najeriya ta Arewa.
Aihaji Dr. Abubakar Imam shi aka fara nad’awa Kwamishinan
jin k’ararakin Jama’a a shekara 1974 a Jihar Kaduna, lokacin ana kiranta Arewa ta Tsakiya. Ya rasu yana da shekara 70 a duniya ranar Juma’a 19 ga watan Yuni, 1981.
Alhaji Abubakar Imam ya rik’a cewa wannan aiki da ya yi, na talifln ‘Magana Jari Ce’ ya yi masa amfani ainun. Ya kan ce wannan aiki shi ne ya ba shi damar zama tare da mashahurin Baturen nan na talifin Hausa, Dr. R.M. East, O.B.E. Ya ce daga gare shine ya koyi duk dan abin da ya koya na game da talifi. Abin mamaki, shi kuma wannan Bature, Dr. East O.B.E., a wajen ‘Mukaddamar’ da ya yi da Turanci tun farkon buga ‘Magana Jari Ce’, ga abin da ya ce: ‘Muna godiya ga En’e ta Katsina, saboda taimakonsu, da hangen nesa da suka yl, har suka yarda, suka ba mu aron Malam Abubakar Imam. suka yarda, ya bar aikinsa, na koyar da Turanci a Midil ta Katsina, ya zo nan Zariya, ya yi wata shida domin ya taimake mu, mu sami wadan nan littattafai a cikin harshensa.
‘Iyakar abin da mu ma’aikatan wannan ofis muka yi, na game da talifin wadannan littattafal, shi ne aiki irin na ofis, na shirya aI’amuran, yadda suka kai har aka buga su. Ban da wannan sal su kuma taimakonsa da muka yi na tattara masa’ littattafai iri iri, don ko zai kwaikwayi wani samfur. Sai fa kuma wajen shiryawa bayan da ya rubuta.
‘Kai, in dai har muna da wani abin da za mu yi kirarin mun yi, game da talifin wadannan littattafai, to, babban abin kirarimmu
kawai, shi ne yadda muka yi har muka binciko wannan malamin’.


MARUBUCI DOKTA ABUBAKAR IMAM (Editan Arewa Na Farko) 1
Alhaji Abubakar Imam, shahararren marbucin Hausa. Wanda ya wallafa littatafai da dama, cikinsu akwai Magana Jari Ce, Ruwan Bagaja da sauransu. Marabucin ya samu shahara a Duniyar Nazarin Harshen Hausa. Ya zamo edita na farko na jaridar Arewa, Gaskiya Ta Fi Kwabo.
Yanzu haka a na nazarin talife-talifen da ya yi a manya da kananan makarantu a Nijeriya.
Tarihin Rayuwarsa
An haifi Alhaji Dr. Abubakar Imam, O.B.E; C.O.N.; LL.D (Hon.) N.N.M.C. a Cikin shekarar 1911 a cikin garin Kagara sa'an nan tana cikin lardin Kwantagora, yanzu kuwa Jihar Neja. [1]Ya yi makaranta a Katsina Training College kuma ya kama aikin malanta a Makarantar Midil ta Katsina a shekarar 1932. Yana da shekara 22 ya rubuta 'Ruwan Bagaja'. Ganin kwazonsa wajen kaga labari mai ma'ana ya sa Dr. R.M. East, shugaban Ofishin Talifi na Zariya, ya roki a bada shi aro daga Katsina ya yi aikin rubuce-rubuce a Zariya. A zaman sa na Zariya ne Abubakar Imam ya wallafa littafin Magana Jari Ce 1-3, Ikon Allah 1-5 da Tafiya Mabudin Ilimi.[2] Abubakar Imam shi ne editan jaridar Gaskiya Ta fi Kwabo na farko kuma shi ne ma ya rada mata sunan ta.
Tasirin Talifinsa Ga Harshen Hausa
Masana/Manazarta Harshen Hausa sun tabbatar da cewar har ya zuwa yanzu babu wani marubuci da ya baiwa Adabin Hausa gudunmowa ta musamman fiye da Alhaji Abubakar Imam, domin kasancewarsa marubuci mai cikakkiyar basira da fasahar shirya labarai iri daban-daban.
Duba da muhimmancinsa ne ma, ya sa masana su ka sanya talifinsa cikin jadawalin darussan Hausa a Makarantun Sakandire da kuma Jami'o'i.
Tunawa Da Shi
Duba ga irin gudunmowa da ya bayar ga Talifi da Aikin Jarida, Masarautar Burtaniya ta girmama Alhaji Abubakar Imam da lambar girma ta O.B.E, Order of British Empire. Daga bisani kuma gwamnatin Nijeriya ta girmama shi ta tata lambar makamanciyar O.B.E, wato C.O.N.
Yanzu haka gwamnatin Jihar KanoTa sanya sunan shi a Babban Asibitin Kula da ma su Yoyon Fitsari, wato Abubakar Imam Urology Hospital, da ke Birnin Kano.
Wadansu littatafan da Alhaji Abubakar Imam ya rubuta sun hada da Tarihin Annabi (S.A.W) Kammalalle da kuma Karamin Sani Kukumi.Hakika,Alhaji Abubakar Imam yana sahun gaba a manyan taurarin adabin Hausa Kuma wanda Har ila yau bashida tamka A Fannin Kaga Labarai