TASKAR KASAR HAUSA

Tshohuwar Taska



 


In Da So Da Kauna


Littafin In Da So Da Kauna na Ado Ahmad Gidan Dabino MON, an fara wallafa shi a shekarar 1991, kenan a yau littafin yana da shekaru 26 da haihuwa.


Labarin In Da So Da Kauna labari ne na soyayya a tsakanin Sumayya da Muhammad. Sumayya yarinya ce kyakkyawa `yar gidan masu hannu da shuni. An yi soyayya irin ta zamanin da, inda Sumayya ta rubuta wa Muhammad wasika a kan irin son da take yi masa, amma da farko Muhammad ya ki, saboda yana ganin sun sha bambam ta fuskar aji, ma`ana ita Sumayya ta fito daga gidan masu arziki, a yayin da shi kuma Muhammad ya fito daga gidan talakawa. 


Manyan taurarin wannan labarin sun hada da: Muhammad, Sumayya, Abdulkadir, Naja`atu, Saratu, Hajiya-Mai-Idon-Cin-Naira.


Farkon harkallar wannan labarin ta faro ne daga inda Sumayya ta hadu da Abdulkadir. A wurin wani biki ne, Sumayya ta hadu da Abdulkadir, saurayi dan gidan masu hannu da shuni. Abdulkadir ya fada cikin soyayyar Sumayya, amma ta ki ba shi hadin kai. A gefe guda kuma ga kakar Sumayya nan Hajiya-Mai-Idon-Cin-Naira, ta kallafa ranta a kan Abdulkadir, saboda tana ganin shi ne ya fi dacewa da ya auri Sumayya a maimakon Muhammad. Daga nan ta shiga neman magani a wurin bokaye domin ta raba Sumayya da Muhammad.


Idan da za a lissafa manyan labarun soyayya na Hausa guda goma wanda ba za a ta6a daina yayinsu ba, to lallai littafin In Da So Da Kauna zai shigo cikin jerin na daya zuwa na uku. Zan iya kwatanta littafin In Da So Da Kauna da littafin soyayya na Ingilishi mai suna Pride and Prejudice na Hausa, saboda tsananin kar6uwarsa.

Wannan littafi na In Da So Da Kauna ya yi tasiri sosai a fagen adabin Hausa, ya zaburar da wasu makaranta na wancan lokacin ta yadda har suka rikide suka koma marubutan kansu, sannan ya samu kar6uwa sosai ta hanyar yaduwa a sassan duniya daban–daban.


An fasara wannnan littafin zuwa harshen Ingilishi  da sunan The Soul of my Heart.

Ga duk wani ko wata mai sha`awar karanta tsofaffin littattafan Hausa, to ya kamata a nemi littafin In Da So Da Kauna a karanta.


A gaida babban yaya Ado Ahmad Gidan Dabino MON. Allah ya ja kwana.



ALLAH SARKI WATARAN


Littafin Allah Sarki Wataran na Fatima Aminu Baba an fara wallafa shi a shekarar 2003 a yanzu littafin yana da shekaru 15 kenan da haihuwa. An wallafa littafin a madaba`ar Al-Amin Bookshop Printing and Publishing Company. Manyan taurarin wannan littafi sun had`a da: Ladidi/Jamila, Malam Munir, Imran, Nuhu, Rahila, Kabir, Munnubiya, Safiya, Yarinye da sauransu.


Littafin Allah Sarki Wataran yana d`auke da jigon soyayya mai tsima rai da tausayi. Ya nuna jajircewa da muhimmancin ilmin `ya mace da zumunci da biyayya ga iyaye.


Ha`ki`ka tarihin rubuce-rubucen littattafan Hausa ba zai manta da wannan gagarumin littafin ba, domin ya k`ayatar a zamaninsa.


Lambun Soyayya


Lambun Soyayya Huce Haushi Asibitin Warke Ciwon So.


Littafin Lambun Soyayya na Mohammad B. Zakari Kafin-Hausa, an fara wallafa shi a shekarar 1994, a yau yana da shekaru 24 da haihuwa kenan. Babu cikakken tarihin madaba`ar da aka wallafa wannan littafi, sai dai sunan Garba Mohammad Bookshop.


Labarin wannan littafi ya faro ne daga wani kirkirarren gari mai suna Mezan – wani gari a gundumar Bulangu can cikin yankin karamar hukumar Zaman. Labari ne irin na Fulanin karkara wanda zai burge mai karatu ta yadda zai ji yadda ake kiwo da noma da rayuwar al`adun Fulani da camfe-camfe.


Manyan taurarin labarin nan su ne: Tijjani da Danjuma, sai Zainab da Zara; wadannan samari da `yammata fa sun buga soyayya ta gani ta fada. An raira wakoki har guda biyu na soyayya a wannan littafi kamar yadda ta kasancen al`adun marubutan wancan lokacin.


Idan har batun al`adun Hausa/Fulani ake nema to littafin Lambun Soyayya ya yi zarra.

Wa Ya San Gobe?


Suleiman ya fid da gilas din da ke fuskarsa ya kafa wa Fatima ido, sannan ya ce, “Fatima me ke tsakaninki da Ahmad?” 


A nan Fatima gwiwarta ta yi sanyi. 


Ya fid do daya daga cikin wasikunta da take rubuta ma Ahmad, ya sake tambayar ta, “Wannan rubutunki ne?” 


Kanta a sunkuye ta amsa , “E.”


Ya yi mata tambayar da ba ta son a yi mata, babu ma kamar daga wajen shi jan gwarzon Suleiman. Idanuwan da take jin tsoro a da, yanzu babu komai cikinsu illa tsabar so da kauna, ya yi tambayar cikin murya mai ban tausayi da al`ajabi ya ce, “FATIMA KINA SON AHAMD HAR ZUCI?”


Fatima zuciyarta ta kara mata kunci, tsananin son Sulaiman ya sake dirar mata da jin tausayinsa a zuci, wanda ba ta da maganinsa kazalika shi ma Sulaiman domin uwa daya uba daya ya fi karfin wasa, ba su da abin yi illa dai hakuri. Ta sake daga ido ta dubi Sulaiman ya yi mata kallon da ba za ta manta ba har. . .


Wannan shi ne dan karamin tsokacin wannan tsohon littafin na Wa Ya San Gobe.

Littafin Wa Ya San Gobe na Bilkisu Salisu Ahmad Funtuwa, an fara wallafa shi a shekarar 1996, kenan a yau littafin yana da shekaru 22 da wallafawa. An buga shi a madaba`ar City Bookshop,a Jakara cikin jihar Kano.


Wannan littafi dai labarin rayuwar soyayya ne da zamantakewar iyali, an yi gwagwarmaya mai tsawo a kan auren jarumar littafin Fatima, a tsakanin wasu masoya – Ahmad, Suleiman da Dokta Na`im. An nuna amfanin ilmin `ya mace da al`adun Hausawa wurin nuna dattako ko akasin haka a yayin neman aure. Littafin ya fadakar kwarai, kuma ya yi dadi ta fuskar nishadantawar.


A gai da marubuciya Bilkisu Salisu Ahmad Funtuwa.

Amintacciyar Soyayya


Littafin Amintacciyar Soyayya na Dan`azumi Baba Chediyar `Yan Gurasa yau shekarunsa 26 da wallafawa. Ba mu da tarihin ko an sake buga shi i zuwa yanzu. An fara bugawa a shekarar 1991. Daya ne daga cikin littattafan kungiyar marubuta ta Raina Kama.


Amintacciyar Soyayya labari ne irin na dauri. Ma`ana labari ne wanda aka gina shi a kan bangon tarihi, a wani gari mai suna Dasura mai tsohon tarihi. Manyan taurarin da suka taka muhimmiyar rawa a wannan littafin su ne: Sarkin Alkamata da matarsa Shaharatu da `yarsu Hamiliya da Alusha wanda ya kasance talakan Sarki Alkamata ne, amma a fagen soyayya ya ciri tuta, ya zama sarki a birnin Dasura, inda ya kasa samari masu takama da abin kansu su goma sha daya a wajen auren Zurfa`a sarauniyar kyau a zamaninta.


Bayan Alusha da Zurfa`a sun yi aure sai suka haifi da, aka sanya masa suna Amil, Amil ya girma ya zama jarumin labarin Amintacciyar Soyayya, ya hadu da Hamiliya `yar Sarki Alkamata suka fara soyayya mai cike da gwagwarmaya.

Mawallafin littafin Dan`azumi Baba Chediyar `Yan Gurasa ya yi doguwar godiya ga mutanen da suka taimaka wajen wallafar wannan littafin, kamar su Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya da Alhaji Garba Baban Ladi Satatima (Bardan Madakin Kano); da sauran `yan uwa da aminan arziki.


Amintacciyar Soyayya littafi ne da za a dade ana tunawa da shi a fannin littattafan Hausa na farko. Ga duk wani mai sha`awar son karatun tsofaffin littattafai ya kamata ya karanta Amintacciyar Soyayya.



Wa Ya Fi Kishi


Littafin Wa Ya Fi Kishi na Rahma Abdulmajid ya shahara, Tsohuwar Taska ba ta da takamaimai tarihin bugun wannan tsohon littafi, saboda babu rubutun shekarar da aka wallafa shi a cikin littattafan. Amma a hasashen filin Tsohuwar Taska wannan littafi kila an fara buga shi a shekarar 1996. Idan kuwa haka ne, to a yau littafin yana da shekaru 21 da haihuwa kenan. Cikin mutanen da suka yi dawainiyar wannan littafi har da shahararren mawallafi Bala Anas Babinlata. An buga wannan litafi a madaba`ar Sauki Publishers da City Publishers Jakara, dukkansu a cikin birnin Kano, karkashin jagorancin kungiyar Raina Kama.


Wannan littafi yana tsokaci a kan dabi`ar kishi, wacce har zuwa yau wasu ke kallon ta a matsayin halitta ce, a halittar ma har yanzu wasu na kallon ta a matsayin halittar da ta ke6antu ga jinsin mata kawai ban da maza. Amma a littafin Wa Ya Fi Kishi an nuna cewar kishi na kowane jinsi ne – maza da mata, sai dai littafin ya kare da ayar tambaya ga makaranta a kan wane ne ya fi kishi a tsakanin jaruman littafin? `Dahir ko Binta? Baya ga kishi da ya zama jigon wannan tsohon littafi, an baibaye jigon da wasu kananun jigogi da suka kara wa labarin armashi, kamar munafurci, soyayya, kissa, zagon kasa, zumunci da tausayi.


An tsara wannan labari ne a wani kirkirarren gari mai suna Amra. Manyan taurarin wannan labari sune:  Muhammad `Dahir da Binta, sai Nafisa da Abubakar da Amina da Musa Bejin da sauransu. Tun a farkon gabatarwar da aka yi wa `Dahir an kwantata shi a matsayin mutum mai tsananin kishi, ta kai ma har saboda tsananin kishinsa kwata-kwata ba ya sha`awar yin aure, don ganin babu macen da za ta iya da halinsa. A gefe guda kuma ita ma Binta nata kishin ba baya ba ne – tara ce take bugun goma ita da mijinta `Dahir. Ta wani 6angaren ma har kishinta yana neman ya zarta na mijinta. 


Wa Ya Fi Kishi shi ne littafi na farko na marubuciyar, amma an gwada basira da kwarewa kamar na tsohon hannu a harkar rubuce-rubuce. Akwai tasirin dabi`un sojoji a cikin littafin, kamar irin wurin da aka an ambaci wani tauraro mai suna Manjo Janar Usman da ya zo wurin Abubakar a cikin littafi na uku, sai a littafi na daya inda ake gabatar da iyalan gidan Alhaji Ibrahim Kamfani, nan ma an yi bayanin babbar `yar Alhajin mai suna Sumayya wacce take auren wani babban hafsan soja.


Marigayi Nasir Ishaq ne ya yi zanen bangon littafi na biyu. Littafi na daya da na uku kuma ba mu da tarihin wanda ya yi zanensu, sai dai kowane zane ya yi daidai da ma`anar labarin cikin littafin.


Wa Ya Fi Kishi ya rubutu, ga duk wani mai sha`awar karatun tsofaffin littattafai ya kamata ya nema ya karanta.



T S O H U W A R  T A S K A 


Kwabon Masoyi


An buga wannan littafin a shekarar 1992, kenan a yanzu yana da shekaru 25 da wallafawa, yana dauke da lambar ISBN kamar haka: 978-309228-6-3. Wannan tsohon littafi ya yi tsokaci game da son abun duniya da yin hannunka mai sanda ga iyaye mata da suke daukar `ya`yansu tamkar wata haja yayin aurar da su, kamar yadda ya faru a tsakanin Jummai da mahaifiyarta Safiya.


Bala da Jummai su ne jaruman wannan littafi, sai Jamilu dan gata – dan gidan Alhaji Bakaki yayin da Asabe da Magaji suke rufa musu baya. Wannan labarin soyayya yana cikin labarun Hausa na farko da aka yi su irin na `yan makaranta, ma`ana soyayya na gudana a tsakanin dalibai. Abubuwan da za su burge mai karatu shi ne yadda dalibai ke tseren shiga ajujuwansu. Littattafansu. Yunifom. Jakunkuna. Jarrabawa. Kada kararrawa, shugabannin dalibai. Gudun makara da yadda dalibai suka yi kungiya suka je suka dubo jikin Bala lokacin da ya kwanta rashin lafiya da sauransu. Ko daga zanen hoton bangon littafin nan za a gane haka.


Bayan haka, wannan littafi zai nuna wa mai karatu cewa an dade ana matsalar wutar lantarki a Nijeriya, saboda yadda marubucin ya kaurara bayani game da dauke wuta. Misali a shafi na 3, an nuna Bala da abokinsa Magaji suna hira kamar haka:


“Ina cikin goge wa Baba kayansa ne fa jiya kawai sai na ga wani haske fal – shi kenan sai na ji mudus. Me za ka ce a nan yanzu?”


Magaji ya girgiza kai ya ce, “Kai dai mu je ka kar6a kawai.”


A shafi na 33 kuma, ga irin abin da ya faru shi ma game da wutar lantarki:


Jummai ta girgiza kai ta ce, “Babu shakka zan yi kokarin gani ni ma, amma fa Allah ya sa muna da wuta kada a dauke mana don na ga kwanan nan da magariba ta yi sai su dauke sai wajen sha biyu su dawo da ita.”


Har wa yau, littafin ya nuna yadda tattalin arzikin Nijeriya ya lalace a tsakanin shekaru 25. Misali a shafi na 26, mun ga inda Jamilu ya ba wa yaro dan aike kyautar Naira biyar ladan kira masa Jummai da ya yi. Naira biyar kuwa kudi ne masu yawa a wancan lokacin.


Kwabon Masoyi na Adamu Mohd ya rubutu, kuma yana cikin littattafan Hausa na farko-farko.



Labarin So/Santsin Soyayya


Littafin Labarin So/Santsin Soyayya na Zuwaira Isa ya shahara a lokacinsa. An fara buga shi a shekarar 1995. Yau shekarunsa 22 cif-cif kenan da wallafawa. An wallafa wannan littafi a madaba`ar City Publishers Jakara Kano. An shimfida soyayya mai gardin gaske a wannan littafin. Asalin sunan littafin na farko shi ne Labarin So, a na biyu sai ya koma Santsin Soyayya (Ci gaban Labarin So) daga nan kuma sai aka yi Santsin Soyayya 2 da 3, idan aka hada gaba daya sun koma littattafai guda hudu kenan. 


Mannir Falalu Bambaro Abokin Doki.


Wannan shi ne take da kirarin da ake yi wa wannan kyakkyawan jarumin wannan labarin soyayyar, an koda wannan jarumi wurin isa da kyau, ta yadda zai iya yin kankankan a tsakanin Salman Khan da Tom Cruise. Hakika marubuciyar ta yi matukar kokarin kirkirar wannan jarumi ta yadda komai ya yi sai ya burge mai karatu, musamman ma idan yana buga wasan kwallon doki, abin da ya kware a kai. Yana daya daga cikin taurarin littafin wadanda suke makalewa a zuciyar mai karatu, bayan an kare karanta littafin.


Mannir Falalu ya yi soyayya da `yammata biyu – ya da kanwa – Zainab da Fatima, ba tare da ya sani ba. Ya hadu da Zainab a wurin wasan kwallon dawaki, a gefe guda kuma mahaifiyarsa tana son kulla zumuncin aure a tsakaninsa da Fatima diyar aminiyarta – kanwar Zainab. Wannan shi ake kira cankacakare mutuwar gaban almuru!


Zainab likita ce, Fatima kuma lauya ce, Mannir kuma dan kwallon polo. Makaranta da yawa a wancan lokacin suna cewa wannan littafi ya yi kama da fina-finan Indiya, amma har zuwa yau dai ba mu da wata takamaimiyar hujja da ke nuna hakan. Kila sai dai mu ce tasirin sinimar Indiyawa kawai, kamar yadda ake raira waka a tsakanin saurayi da budurwa. Sarkakiya, ta`ammuli da miyagun kwayoyi da sauransu. Duk ire-iren wadannan abubuwa sun bayyana a cikin wannan littafin. Littattafan marubuciyar na baya da na gaban Labarin So/Santsin Soyayya sun fitar da tsantsar fasahar Zuwaira Isa. 


Marubuciyar wannan shahararren littafi, Zuwara Isa, idan har ba ta zama ta farko ba a wajen fito da samfurin canja sunan littafi ba, alhali labari guda ne, to lallai za ta zama ta biyu a tarihin rubuce-rubucen Hausa. Kuma tana daya daga cikin marubutan da suke kirkirar sunayen garuruwan labarin littattafansu, kamar a cikin wannan littafi, mai karatu zai ji garuruwa irin su Disina, Lantana da sauransu. Kuma tana da kwarewar yin amfani da tantagaryar Hausa, da zambo da fikirar harshe da barkwanci. Hakika duk wani mai sha`awar kwaikwayar yadda ake amfani da kaifin harshe wurin iya magana, to ya nemi littattafan Zuwaira Isa ya karance su. Ga mai sha`awar tsofaffin littattafan Hausa kuma shi ma kada a bar shi a baya, a nema a sha labarin tsohuwar alawa irin ta da.



KULU


Kulu littafin Bala Anas Babinlata an fara buga shi a shekarar 1992 da 1993. An wallafa shi a madaba`ar Jigon Hausa Publishers. A yau shekarun liitafin 25 da wallafawa kenan. Kusan dukkan littafi yana da alkibla, watau wani sako da zai isar ga jama`a don fadakarwa ko jan hankali ko yin nuni cikin nishadi. Wannan littafi na Kulu yana dauke da sako ga matasa musamman a kan karatunsu, ta yadda matasa suke nuna dabi`ar kyamar yin kananun sana`o`i kawai saboda sun yi ilmi mai zurfi ko don dalilin sun yi rayuwar jami`a, sai ka ga matashi ya dage shi a dole sai ya ji dadi, sai ya shiga ofis da dai sauransu. Darasin wannan littafi zai koya wa mutane dogaro da kai ta hanyar amfani da ilimin da muka samu ba wai lallai sai an yi aiki da gwamnati ba ko wata hukuma.


Manyan taurarin cikin wannan littafi sun hada da: Dahiru, Alawiyyatu, Kulu, Alhaji Halliru. Badakalar wannan labari za ta burge mai karatu, ta yadda ake gumurzun soyayya a tsakanin Dahiru – direban gidan Alhaji Halliru da `ya`yansa Kulu da Alawiyyatu. Dahiru na son Kulu amma ita ba ta son sa, a yayin da Alawiyyatu kuma ta mato a cikin sonsa. Sauran labari sai an nutsa cikin wannan littafi mai tsohon tarihi.


A karshen littafi na biyu, marubucin ya yi wani dan tsokaci game da makaranta da suke damun sa a kan a wallafa littafi na uku. Marubucin ya kawo dalilai da dama da yake ganin babu bukatar yin hakan. Ya rufe da wata sadara da yake fadin cewar,


 “Yayin da ka tunkari mace da sunan soyayya in ta ce a`a to rabu da ita sai Allah ya turo maka mai sonka amma in ka nace, rashin son da take yi maka zai ci gaba ne da bunkasa har ya zama tsana mai tsanani. In kuwa ka bari mace ta tsane ka sai dai Allah ya kiyaye.”


Kulu shi ne littafin babban marubuci Bala Anas Babinlata na farko. Ga duk wani mai sha`awar fara karatun littattafan Babinlata to yana iya farawa da littafin Kulu.



Allura Cikin Ruwa


Littafin Allura Cikin Ruwa na Bilkisu Salisu Ahmad Funtuwa yau shekarunsa 23 da fitowa. Shi ne littafin marubuciyar na farko. An fara buga shi a shekarar 1994, a kamfanin dab`i na Gidan Dabino Publishers. Yana dauke da lambar ISBN wanda a lokacin ba kowane littafi ba ne yake dauke da shi. Wannan littafi na Allura Cikin Ruwa yana da tsaho, don haka an karkasa shi zuwa juzu`ai uku. Littafi na farko yana da shafi 96, na biyu yana da 87, na uku kuwa yana da 107.


A wannan littafi an shirya labari mai gardin gaske, da ake tattaunawa yawu na zuba don dadi. Tsagwaron soyayya ce aka shimfida tsakanin masoya da suke karakaina a kan masoyiya “Asiya” da kowa ke fatan ya zarci dan`uwansa. An sarke wannan soyayya da rigingimun cikin gida musamman na bambancin gidaje da na zaman unguwa da abokan hamayya, wadanda suka shiga ciki suka yi dame-dame.


“Ni Asiya Yusuf mutuniyar Malumfashi ce a anguwar Kofar Fada. . .” wadannan su ne kalmomin farko na littafin Allura Cikin Ruwa, wadanda za su ja hankalin mai karatu ya ji son sha`awar karanta labarin.


Wadanda suka tace suka duba suka ya yi gyare-gyaren wannan littafi kafin a kai ga madaba`a, sun hada da Farfesa Saidu Muhammad Gusau na Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, a jami`ar Bayero ta Kano, a lokacin yana Dokta.


Wannan littafi dai har yanzu yana nan a kasuwa ga duk mai sha`awar son karanta shi.



An buga wannan littafin a shekarar 1990, an sake bugawa a 1992 da 1995 da 2001 da 2006. Alhaki Kuykuyo Ne labari ne mai nuna karshen duk wani azzalumin magidanci mai musguna wa iyalansa, kamar yadda ya faru da Alhaji Abdu. Inda ya musguna wa matarsa Rabi da `ya`yanta, ya auro tsohuwar kilaki Delu, daga karshe ya kori Rabi da `ya`yanta. Alhaki Kuykuyo Ne ya biyo Alhaji Abdu har gida, inda rumfunan kasuwanninsa suka kama da wuta, ya kama Delu da yaronsa Jatau suna cin amanarsa.


Alhaki Kuykuyo Ne shi ne littafin Hausa na zamani na farko da aka fassara shi zuwa harshen Ingilishi. Inda wani kamfani mai suna Blaft Publishers a kasar Indiya suka fassara shi, aka sanya masa suna (Sin is a Puppy that Follows you Home) a shekarar 2012. Bayan bugun takarda har da na lataroni irin wanda ake cewa ebook na kamfanin Kindle, wanda aka dinga sayar da shi a farashin ($4.99)


Alhaki Kuykuyo Ne ya samu kar6uwa sosai a kasar Indiya, inda har wasu jaridu suka yi sharhi a kan littafin da tasirin fina-finan Indiya a Nijeriya. Har wa yau, Alhaki Kuykuyo Ne shi ne littafi na farko daga nahiyar Afrika da aka ta6a bugawa a kasar Indiya. An yi rubuce-rubuce da bincike na ilmi tun daga matakin digiri na farko har zuwa na uku a kan wannan littafin. Novian Whitsitt ya yi binciken digirinsa na uku (Phd thesis) a kan littafin Alhaki Kuykuyo Ne a shekarar 2002. Farfesa Abdallah Uba Adamu na jami`ar Bayero ta Kano ya yi rubutu a kan shirin fim din littafin a cikin littafinsa mai suna: Transglobal Media: Flows and African Popular Culture.


A shekarar 1998 Abdulkareem Muhammad ya mayar da Alhaki Kuykuyo ne zuwa shirin fim din Hausa. Wani abu da yake burge ni da littafin nan shi ne, yadda yake nuna mana ta6ar6arewar tattalin arzikin Nijeriya na shekaru ashirin baya. Idan muka dubi yadda Alhaji Abdu yake ba wa Rabi N5 a matsayin kudin abinci ita da `ya`yanta guda tara, shi kuma ya je ya kashe sama da N10 a gidajen abinci da wurin karuwai.


A lokacin da yawancin littattafanmu suke kulle a cikinmu Hausawa kadai, ba sa iya ko tsallakawa harshen makwabtanmu, Alhaki Kuykuyo Ne ya ciri tutar samun `yancin yin nutso a cikin duniya.



~*T S O H U W A R  T A S K A*~


Hannunka Mai Sanda


Littafin Hannunka Mai Sanda na Aminudeen Amadu Yaro Kauran Namoda, an wallafa shi a shekarar 1995, yau shekarunsa 22 kenan da wallafawa. An buga wannan littafi a kamfanin Gidan Dabino. Littafin yana dauke da lambar ISBN kamar haka: 978-2149-21-7. Wanda ya duba ya tace littafin nan shi ne Farfesa Sa`idu Muhammad Gusau a lokacin yana matsayin dokta.


Hannunka Mai Sanda littafi ne wanda ya kunshi nasihohi cikin fasalin hikayoyi da almarori. An tsara labaru ne masu ban sha`awa wadanda zukata ke bukata tun ma ba a lokacin jimami da alhinin kadaitaka da saka yin tunani kan al`amuran yau da gobe ba. Wannan littafi yana cikin littafin gajerun labarai na farko-farko da aka fara wallafawa a Hausa – a lokacin da duniyar adabin kasuwar Kano ta ta`allaka a kan dogon rubutun zube. Kowane labari yana magana a kan wani batu na daban mai yin fadakawar, littafin yana dauke da wasu isharori da suka hada da:


Nuna muhimmancin ilmi.


Fito da kyawawan al`adu da kuma nuna aibin munanansu


Ishara game da aure da wasu sigoginsa


Bambancin jahili da mai ilmi ko masani.


Hakkin makwabtaka.


Mai hakuri yana tare da Allah.


Littafin yana dauke da labaru guda takwas sun hada da:


Zaman Makwabtaka


Zama Da Madaukin Kanwa


Hakuri Maganin Babu


Labarin Wani Makaho Da `Ya`yansa


Mai Hakuri Yana Tare Da Allah


Zaman Kishiya Da Kishiya


Zaman Jahili Da Mai Ilmi


Sharri Kare Ne Mai Shi Yake Bi.


Mawallafin wannan littafi – Aminuddeen Alhaji Ahmadu Yaro, an haife shi a garin Kauran Namoda cikin tsohuwar jihar Sakkwato a daidai shekarar 1975. Ya yi karatun firamarensa a Namoda Model firamare, sannan ya yi karatun sakandire a Namoda, dukkansu da ke garin Kauran Namoda. 


Har wa yau, wannan littafi yana dauke da zane irin na karin bayani a kan kowane labari, domin mai karatu ya samu saukin ganewa. Wanda ya yi wannan zane shi ne marigayi Nasir Ishaq Dan Aljan.