Bikin ya gudana ne a makarantar firamare ta Herwagana da ke garin Gombe a ranar Asabar 27 ga watan Augustar 2022, inda aka sami halartan jiga-jigan masana a harkar rubutu da masu yi wa Adabi hidima irin su; Alhaji Salihu Abdullahi (Jarman Kumo) wanda ya yi sharhi a kan littafin Siyasa Ba Da Gaba Ba. Sai Malam Dalhatu El-Nafaty wanda ya yi tsokaci a kan rubuce-rubuce a wannan zamani. A yayin da Malam Ibrahim Lamiɗo PhD wanda malami ne a jami'ar tarayya da ke Kashere, ya jaddada goyon bayansa ga marubutan tare da ƙarfafa musu guiwa. Sai Alhaji Kabiru Ibn Muhammad (Sarkin Doya) shugaba kuma babban daraktan gidan rediyo da talabijin mallakar jihar Gombe DG GMC shi ma ya yaba wa marubutan tare da jaddada goyon bayansa gare su.
TASKAR KASAR HAUSA
Saturday, 3 September 2022
TASKAR ƘASAR HAUSA TA JAGORANCI BIKIN ƘADDAMAR DA SABBIN LITTATAFAN ADABI A JIHAR GOMBE
Littatafan da aka kaddamar sun haɗa da; Siyasa Ba Da Gaba Ba wanda marubuta goma sha ɗaya suka yi hadakar samar da shi, sai Lu'ulu'u A Cikin Juji da Duniyar Audu na Rufai Abubakar Adam (R.A Adam), sai littafin Fitinar Zamani na Adamu Ahmed Yarma.
Daga ƙarshe an bayar da kyaututtuka ga marubutan da kuma manyan mutanen da suka halarci taron.
JERIN SUNAYEN MARUBUTAN DA SUKA RUBUTA SIYASA BA DA GABA BA
1. Rufai Abubakar Adam (R.A Adam)
2. Adamu Ahmed Yarma
3. Ayuba Muhammad Kumo
4. Ahmad Usman El-Nafaty
5. Usman Abubakar (Usman Flash)
6. Shehu T. Abdullahi
7. Rashidat Muhammad (Queen Rashoo)
8. Zainab Hussaini
9. Aishatu Ibrahim Yahaya
10. Usman Umar Assakaafiy
11. Sunusi Musa
Friday, 10 September 2021
Barka Da Zuwa
Shafin
Taskar Kasar Hausa
Domin Raya Adabin Hausa
Tallata Addini Da Al'ada
Adana Tarihin Kasar Hausa (Jiya da Yau)
Adana Littafan Hausa PDF
Bincike akan Kasar Hausa
Tattara bayanai da Adana su
MUN SABUNTA SHAFIN TA HANYAR DAURA LITTATAFAN NAZIR ADAM SALIH GUDA (11) DON KU SAUKE CIKIN MANHAJAR PDF
Monday, 12 October 2020
Shahararru Biyar (Famous Five)
Gasar rubutun kagaggun labarai na shekarar 1935 ce ta haifar da wadannan littatafai da Farfesa Abdallah Uba Adamu ya sanya wa suna Shahararru Biyar ( Famous Five), ga su kamar haka;
1. Ruwan Bagaja (Abubakar Imam)
2. Shaihu Umar (Abubakar Tafawa Balewa)
3. Gandoki (Muhammad Bello Kagara)
4. Idon Matambayi (Muhammadu Gwarzo)
5. Jiki Magayi ( Robert East da John Tafida Umar)
Wednesday, 26 August 2020
Tuesday, 27 August 2019
#RananHausa 26 ga watan Agusta 2019
Jinjina ga Mazan Jiya;
1.Dokta Abubakar Imam (Magana Jarice da Ruwan Bagaja).
2.Ado Ahmad Gidan Dabino (Inda So da Kauna).
3. Sir Abubakar Tafawa Balewa (Shaihu Umar).
4. Ahmadu Ingawa (Iliya Dan Maikarfi).
5. Nuhu Bamalli (Mungo Park Mabudin Kwara)
6. Bilkisu S. Funtua (Ki yarda dani)
7. Muhammadu Ingawa ( Ka koyi karatu)
8. Nazir Adam Salih (Kudi da Maciji)
9. Bala Anas Babinlata ( An yanka ta tashi).
10. Abdullahi Mukhtar Yaron Malam ( Bajakade da Yahudu badda Musulmi)
11. Abdul'aziz Sani Madakin Gini (Kundin Tsatsuba)
12. Shehu Usman Muhammad (Mazan Fama)
13. Aliyu Abubakar Sharfadi (Malikus Saifi)
14. Shafiu Dauda Giwa (Ihunka Banza da Gobe Jar kasa)
15. Bashir Yahuza Malumfashi (Babban Tarko).
16. Bashir Usman Tofa (Tunaninka Kamanninka)
17. Ibrahim Malumfashi, Bukar Mada da Danladi Z. haruna (Dare Dubu Da Daya)
18. Balaraba Ramat Yakubu ( Budurwar Zuciya)
19. Hafsatu M.A Abdulwahid (So Aljannar Duniya)
20. Kabiru Yusuf Anka (Kushewar Badi)
2.Ado Ahmad Gidan Dabino (Inda So da Kauna).
3. Sir Abubakar Tafawa Balewa (Shaihu Umar).
4. Ahmadu Ingawa (Iliya Dan Maikarfi).
5. Nuhu Bamalli (Mungo Park Mabudin Kwara)
6. Bilkisu S. Funtua (Ki yarda dani)
7. Muhammadu Ingawa ( Ka koyi karatu)
8. Nazir Adam Salih (Kudi da Maciji)
9. Bala Anas Babinlata ( An yanka ta tashi).
10. Abdullahi Mukhtar Yaron Malam ( Bajakade da Yahudu badda Musulmi)
11. Abdul'aziz Sani Madakin Gini (Kundin Tsatsuba)
12. Shehu Usman Muhammad (Mazan Fama)
13. Aliyu Abubakar Sharfadi (Malikus Saifi)
14. Shafiu Dauda Giwa (Ihunka Banza da Gobe Jar kasa)
15. Bashir Yahuza Malumfashi (Babban Tarko).
16. Bashir Usman Tofa (Tunaninka Kamanninka)
17. Ibrahim Malumfashi, Bukar Mada da Danladi Z. haruna (Dare Dubu Da Daya)
18. Balaraba Ramat Yakubu ( Budurwar Zuciya)
19. Hafsatu M.A Abdulwahid (So Aljannar Duniya)
20. Kabiru Yusuf Anka (Kushewar Badi)
da sauransu. Za muyi kokarin kawo Tarihin wadannan Marubuta da littatafansu, nan gaba in Allah ya yarda.