TASKAR KASAR HAUSA

(PDF) ME YAFI KUDI? (1996) Nazir Adam Salih

PDF Me Yafi Kudi Nazir Adam Salih

ME YAFI KUDI? (1996)

‘Barau!!’ Alhaji Abubakar  ya qwalla wa maigadinsa kira. Shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu. Arangama wanda ke maqale a kan bishiyar dake daf da qafar benen,  ya ji gabansa ya faxi, domin ya san maigadin na iya kawo cikas ga abin da yake shirin aikatawa. Tunaninsa ya katse da ya ji takun Barau yana hayowa benen,  lokaci guda kuma dabara ta faxo masa.
Ko da Barau ya qaraso saman benen daf da in da Arangama ke maqale, sai ya ji wani abu mai kama da aradu ya daki tsakiyar kansa. A take a nan ya baje sumamme, a daidai wannan lokaci sai wutar lantarkin gidon ta xauke, duhu ya mamaye ko ina kamar  maqabarta.

Nazir Adam Salih (1996)